On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

'Karin Wasu 'Yan Matan Cibok Biyu Sun Kubuta Daga Hannun Boko Haram

CHIBOK GIRLS

Shekaru 8 bayan da Mayakan Boko Haram Suka sace Yan Matan Makarantar Sakandirin Chibok 276, A yanzu haka Dakarun Soji masu gudanar da shirin Sumame na Operation Hadin Kai sun Kara samun nasarar Ceto wasu mata Biyu na Makarantar daga cikin Dajin Sambisa.

Rahotanni sun baiyana cewa an kubutar da matan ne a Gazuwa dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno a kwanan nan.

An kubutar da matan, Mariam Dauda da Hauwa Joseph tare da Jariran da suka Haifa, A lokacin da suke bayanin halin da suka tsinci kansu a ciki bayan shafe shekaru 8 a cikin Daji, Yayin wani taron Mamema Labarai da rundunar ta shirya a Barikinta dake Maimalari a Maiduguri a jiya.

Sun baiyana cewa Mayakan Boko Haram din Sun Aure su harma sun haihu tare dasu, Sai dai sun baiyana cewa Dakarun Sojin Kasar nan sun samu nasarar halaka  mazajensu a watannin da suka gabata.

More from Labarai