On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kasar Morocco Ta Amince Da Yin Amfani Da Tabar Wiwi

GANYEN TABAR WIWI

Hukumomin kasar Moroco sun amince sun amince da yin amfani da Tabar Wiwi a masana’antu da bangaren yin magani da kuma yin fataucin ta zuwa kasashen waje.

Hukumomi a kasar sun baiyana cewa Manoman da suke a matsayin kungiya a tsaunikan Al-Houciema da Taunat da Chefchauen dake arewacin kasar, za’a basu izinin noma Tabar wiwi  domin ganin sun biya bukatun bangarori  10 da aka amince ayi amfani da ita.

Dama dai noman Tabar wiwi a kasar Moroco ta haramtacciyar hanya  ba sabon bakon abu bane, sai dai a halin yanzu dokar  da  yan majalisar  dookokin kasar suka amince da ita ta haramta yin amfani da Tabar Wiwi domin jin Dadin jiki kadai.

Dokar dai zata temaka wajen bunkasa kudin shiga da manoman ke samu da kuma kare su daga fadawa hannun dillalan miyagun kwayoyi   wanda suke  safarar  Tabar wiwi  ta haramtacciyar hanya zuwa nahiyar turai.