On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kasashen Amurka da Burtaniya Sun Gargadi Al'ummarsu Mazauna Najeriya Kan Yiwuwar Fuskantar Harin Ta'addanci

Ofisoshin jakadancin Amurka da Burtaniya da ke Najeriya sun gargadi 'yan kasashensu da su yi taka tsan-tsan akan barazanar karuwar hare-haren ta’addanci a Najeriya, musamman a Abuja.

 

A cikin sanarwar da aka  fitar ta shawarwari kan  tsaro a baya-bayan nan, ofishin jakadancin ya shawarci ‘yan kasar ta Amurka da su guji duk wasu  tafiye-tafiye da ba su da mahimmanci, su kasance cikin shiri da kuma gujewa wurare masu cunkoson jama’a.

Sanarwar ta ce koda yake ba’a iyakance takamaimaen wuraren da hare-haren ka iya shafa ba, amma yana  iya shafar gine-ginen gwamnati da  wuraren ibada da  makarantu da kasuwanni da manyan kantuna da otal-otal da  mashaya da gidajen cin abinci da wuraren wasannin motsa jiki da tashoshin mota da wuraren aiwatar da dokada  da kungiyoyin kasa da kasa.

Haka kuma offishin jakadancin na Amurka a Najeriya, ya kara da cewa zai takaita yawan ayyukansa har sai zuwa abunda hali ya yi nan gaba.

Itama, Kasar Burtaniya ta sabunta sanarwar bada shawara kan ayyukan  ta'addanci ga ‘yan kasar a   Najeriya.

Burtaniya, ta yi gargadin karuwar hare-haren ta'addanci a babban birnin tarayya Abuka.

Sanarwar ta kuma shawarci 'yan kasar ta Burtaniya da su kasance cikin shiri, su rika yin la'akari da duk wani motsi da kai komo tare da bibiyar labaran cikin gida da shawarwarin hukumomin tsaro.

Hakazalika, babban offishin jakadancin Biritaniya da ke Abuja yace  ma'aikata masu mahimmanci ne kawai za a ba su damar shiga offishin kuma matakin ya shafi daukacin ma'aikatan.