On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kasashen Angola Da Libiya Sun Yiwa Najeriya Fintikau A Bangaren Hako Danyen Mai

GANGAR DANYEN MAI

Kasashen Angola da Libiya sun kwace kanbun da Najeriya ke rike dashi a bangaren yawan hakon danyen mai, inda suke hako ganga dubu Dari 972 a kowace rana tun daga cikin watan Augustan daya gabata.

Angola tasha gaban Najeriya ta bangaren yawan hako dan mai a cikin watan, kamar yadda kididdigar da kungiyar kasashe masu arzikin fitar  da mai a duniya OPEC ta baiyana.

Kungiyar ta Opec ta baiyana haka ne ta cikin rahotonta na watan Satumba, rahoton ya nuna cewa yawan dan man da Kasar nan ke hakowa ya ragu a cikin watan Augustan bana, inda ya sauka zuwa kasa da Milyan Daya, wanda shine mafi karanci da aka samu a cikin shekarun da suka gabata.

More from Labarai