On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Kason Farko Na ‘Yan Najeriyar Da Suka Makale A Sudan Sun Dawo Gida Najeriya

Kason farko na ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan sun dawo gida Najeriya. An kwaso su ne ta cikin jirgi inda suka sauka filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da karfe 11 da rabi na daren jiya.

‘Yan  Najeriyar  sun samu tarba  ta musamman daga  Ministar  kula da harkokin Jin kai  da kare afkuwar  Bala’oi  ta kasa,Sadiya  Umar  Faruk, sai shugabar  Hukumar kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare, uwargida  Abike  Dabiri  Erewa,  da  shugaban hukumar  Ba  da Agajin gaggawa  ta kasa NEMA, Ahmed Mustapha.

Da  take  yiwa mutanen jawabi, Ministar  ta baiyana cewar  za’a  baiwa  kowane  mutum  guda  naira dubu  100  domin biyan wasu  ‘yan bukatu da suka shafe su.

Ita ma   a nata jawabin,  Uwargida  Dabiri Erewa  ta baiyana cewar  akwai ‘yan Najeriya kimanin milyan ukku a kasar  Sudan, kuma  gwamnati  zata yi  bakin kokarin domin ganin an kwashe  su.

Rahotanni  sun  baiyana cewar  a yanzu haka  jiragin kanfanin Azman da na Max Air  na kan hanyarsu ta zuwa kasar  Masar  domin kara kwaso  ‘yan Najeriyar da  suka  yi  gudun hijira  daga kasar  Sudan, saboda  yakin da kasar  ta samu kanta a ciki.