On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kaura Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Bauchi A Karo Na Biyu

Gwamna Bala Muhammad na jam’iyyar PDP ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Bauchi na 2023

Shugaban tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta Bauchi, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed, shine ya sanar da sakamakon.

Ya ce, Sanata Bala gwamna mai ci kuma Ƙaura Bauchi, shi ne ya samu nasara ne da ƙuri’u 525,280.

Haka kuma, Ya bayyana Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 432,272.