On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kotu Ta Aike Da Amarya Gidan Gyaran Hali A Kano

Wata kotu dake zaune a karamar Hukumar kura a jihar kano ta tisa keyar wata amarya da ta zubawa Abokiyar zamanta tare da ‘yarta mai shekara 4 a duniya Ruwan zafi.

Rahotanni  sun  baiyana  cewa, Amaryar  mai  suna  Maryam  Abdurrahman  Chiromawa   ta aikata  Danayen  aikin  ne,  a lokacin  da  kishiyar  ta ta  ke  tsaka  da  bacci

Har  ila  yau,  mai Laifin  ta  amsa  Laifin  da  ake  tuhumarta  da  aikatawa. 

Wakilinmu Ado ‘Danladi Farin Gida ya rawaito alkalin Kotun  Aminu Usman Fagge ya dage cigaba da shari’ar zuwa mako uku na gaba lokacin da ake fatan Matar da aka watsawa ruwan zafin zata smu sauki tare da diyarta.

More from Labarai