On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kotu Ta Ayyana Muhammed Abacha Amatsayin 'Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam'iyyar PDP

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a yau Alhamis ta tabbatar da Mohammad Sani Abacha amatsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano

Alkalin kotun mai shari’a A.M Liman a wani hukunci da ya yanke a yammacin yau ya soke zaben fidda gwanin da ya tsaida  Sadik Amunu Wali a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP tare da umartar INEC da ta maye gurbin  sunansa da sunan Muhammad Sani Abacha. 

Tunda farko an tsara yanke hukuncin ne da misalin karfe 12  na rana a yau amma daga baya aka canza zuwa karfe 4:00 na yamma.

 Kotun ta amince da dukkan rokon wanda ya shigar da kara Mohammed Sani Abacha akan Sadik Aminu Wali da  INEC da Kuma jam'iyyar PDP.