On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Bada Umarnin Jefe Wasu Mutane Ukku A Jihar Bauchi

KOTU

Wata Kotun Shari’ar Musulunci dake jihar Bauchi Ta yankewa wasu mutane Ukku Hukuncin Kisa ta hanyar jefewa, sakamakon cin zarafin wasu Kananan Yara maza biyu, bayan sun basu kayan maye.

Wani Jami’in Hukumar Hisba dake Jihar Bauchi, Adamu Dankafi  Ya fadawa kotun dake Ningi  Yadda  Mutanen Ukku suka hada baki wajen aikata lefukan a lokacin da ake yi masu tambayoyi a gaban kotu.

Ya kuma kara da cewa, an kama mutanen ne  a kauyen  Gawada a cikin watan Mayun Bana sakamakaon Korafin da Iyayen yaran suka shigar na cewar  mutanen  sun bawa yaransu kayan maye.

Adamu Dan Kafi, Ya kara da cewa Mutanen masu shekaru 20 zuwa 70 basu samu wani lauya da zai kare suba a lokacin da aka gabatar da shari’ar, inda ya baiyana cewa suna da wa’adin  wata  Daya domin su daukaka kara.

More from Labarai