On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Bada Umarnin Tsare 'Dan China Da Ake Zargi Da Kisan Ummukulthum

Babban Kotun Majistare A Jihar Kano Ta Bayar Da Umarnin Tsare Geng Quarong 'Dan Kasar China Da Ake Zargi Da Kisan Ummukulsum Buhari.

Mai Shari'a Hanif Sanusi Chiroma Itace Ta Bayar Da Wannan Umarni Bayan Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano Ta Gurfanar Dashi A Gaban Kotun Da Safiyar Ranar Laraba.

An gurfanar da shi ne a kotun mai  lamba 30 dake zungeru A Kano.

Lauyan Gwamnati Barista Khalifa Auwal Hashim ya fadawa  kotun cewa, bata da hurumin sauraren ƙarar , kasancewar laifin da ake tuhuma da  babban laifi ne.

Ana zargin Geng dan shekara 48 da aikata laifin kisan kai ta hanyar amfani da wuƙa wajen yiwa  Ummulkursum 'yar shekara 23 mugagan raunuka  wanda hakan yai sanadin mutuwarta.

Kotun ta tsaida ranar 13 ga watan Oktoba 2022  domin samun shawarwari daga ma'aikatar Shari'a ta  Kano tare da bada umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali zuwa lokacin da za a dawo zaman na gaba.