On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Daure Wani Jigon Jam'iyyar APC A Jihar Legas Saboda Laifin Sayen Kuri'u A Zaben 2023

Wata babbar kotun jihar Legas da ke zamanta a Ikeja ta yanke wa wani shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Surulere, Wahab Hammed hukuncin daurin shekara daya a gidan yari.

Mai shari’a Ismail Ijelu ya yanke wa wanda ake kara hukuncin ne bisa laifin siyan kuri’u  bayan ya same shi da laifuka biyu da suka hada da hada baki da cin hanci.

Lauyan hukumar EFCC, Samuel Daji, ya shaida wa kotun cewa a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wanda ake tuhuma ya hada baki da wani Segun Ijitola wanda har yanzu bai je gaban kotun ba, wajen aikata cin hanci da rashawa da  masu kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya na 2023.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Ijelu ya yanke wa Hammed hukuncin daurin shekara daya ko kuma tarar Naira milliyan 1.