On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Hana Hukumar Zabe Tsayar Da Rijistar Katin Zabe.

A Yaune Mai Shari’a Mobolaji Olajuwon na Babbar Kotun Taraiyya dake zamanta a Abuja, Ya Dakatar da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zamanta Kanta, Daga dakatar da aikin rijistar katin Zabe a ranar 30 ga watan Yunin da muke ciki.

Mai shari’a Olajuwon Ya bayar da umarnin ne na wucin gadi, biyo bayan  karar da Kungiyar nan mai rajin Kare Hakkin Dan Adam  SERAP ta shigar a  gaban kotun.

A farkon watan da muke ciki ne, Kungiyar ta SERAP da Daidaikun wasu ‘yan kishin kasa 185  suka kai karar Hukumar Zabe ta kasa INEC, Inda suka bukaci Kotun ta aiyana matakin  dakatar da aikin rijistar Katin zaben,a matsayin wanda ya sabawa doka, Sannan  kuma gazawa ce ga hukumar wajen bawa Yan Najeriyar da suka kai Munzali damar yin amfani da yancin da suke dashi.

Daga bisani an dage  shari’ar zuwa ranar 29 ga watan da muke ciki domin cigaba da zaman shari’ar.