On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Hana Kamawa Ko Gayyatar Ganduje Da Iyalansa Ko Mukarraban Gwamnatinsa

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin wucin gadi na hana rundunar ‘yan sandan Najeriya da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa, musgunawa ko kamawa ko gayyata, ko kuma tsare tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da iyalansa  ko duk wani wanda ya taba nadawa mukami yayi aiki a karkashin gwamnatinsa.

Hakazalika kotun da Mai shari’a A.M Liman ke jagoranta ta Bada umarni ga wasu mutane shida da ake kara.

Umurnin zai ci gaba da aiki har sai an saurari karar da kuma tantance ainihin abun da ya samo asali.

Kotun ta yanke hukuncin ne  biyo bayan karar da Barista B. Hemba ya shigar a gaban Kotun, amadadin tsohon gwamnan jihar Kano.

Mai shari’a Liman ya kuma sanar da cewa umarnin na wucin gadi zai ci gaba da kasancewa har sai an saurari bukatar masu Kara a ranar 14 ga Yuli na 2023.