On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta Tabbatar Da Bashir Machina A Matsayin Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa A Jam'iyyar APC

Bashir Machina

Babbar kotun taraiyya dake zamanta a jihar Yobe ta sake tabbatar da Bashir Machina a matsayin Dan Takarar majalisar dattawa Mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin Jam'iyyar APC.

Kotun Mai zamanta a Yobe ta sake tabbatar da Bashir Machina a matsayin Dan takarar kujerar majalisar dattawa Mai wakiltar Yobe ta Arewa karkashin Jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.

Idan ba'a manta ba Bashir machina ya turje akan kin baiwa shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan takarar bayan Kayen da ya Sha a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar APC, Wanda Bola Tinubu ya samu nasara.

Daga baya Jam'iyyar APC ta aike da sunan Ahmed Lawan a matsayin Dan Takarar ta, Amma Kuma Machina, ya bijirewa yin hakan, kasancewar Sanata Ahmed din ba shiga takarar Sanata ba.

A yanzu haka Babu sunan shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan cikin jerin sunayen yan takara da Hukumar Zabe ta Kasa ta fitar.

Zamu kawo maku cikakken labarin a nan gaba....