On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Tabbatar Da Bashir Machina A Matsayin Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa

BASHIR MACHINA DA SHUGABAN MAJALISAR DATTAWA SANATA AHMED LAWAN

Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, Ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin halastacen dan takarar sanatan Yobe ta Arewa, a karkashin jam’iyyar APC.

Kotun ta goyi bayan hukuncin da kotun daukaka kara dake zamanta a birnin Damaturun jihar  Yobe  ta yanke tun a lokacin baya,  wanda  ta baiyana cewar, shugaban majalisar dattawa  sanata  Ahmad Lawan, ba shine halastaccen dan takarar  jam’iyyar  APC  akan matsayin ba.

Kotun daukaka  Karar  ta baiyana cewa, kasancewar  Sanata Ahmad Lawan bai shiga  zaben fidda  gwani na dan takarar sanatan da aka yi a ranar 28 ga watan Mayun bana, a saboda haka  ba  halastaccen  dan  takara ba ne.

Kotun mai alkalai Ukku, karkashin mai shari’a Monica Dongban Mensem , Ta baiyana cewa, zaben fidda  dan takarar sanata da jam’iyyar APC ta kara yi a ranar  9 ga watan Yunin bana, haramtacce  ne  kuma ya sabawa  kundin tsarin mulkin kasa.

More from Labarai