On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Tabbatar Da Christopher Maikalangu 'Dan Takarar Jam'iyyar PDP Amatsayin Shugaban Karamar Hukumar Kwaryar Birnin Abuja da Kewaye

Wata kotun birnin tarayya Abuja ta tabbatar da zaben Hon. Christopher Maikalangu, dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin shugaban karamar hukumar kwaryar birnin Abuja da kewaye.

A hukuncin da aka yanke, kotun mai alkalai uku ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a ranar 5 ga watan Agusta, wadda ta bayyana Hon. Murtala Usman Karshi na jam’iyyar  APC   a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 12 ga watan Fabrairu.

Alkalan sun ce hukuncin da karamar kotun ta yanke ba rashin ka’ida ba  ne kawai, ya nuna gazawar da duk nasarorin da aka samu a dimokuradiyyar Najeriya.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan yanke hukuncin, Shugabankaramar hukumar da kwaryar binin Abuja, Christopher Zakka Maikalangu, ya ce bangaren shari’a shi ne fata na karshe ga talakawa, yana mai godiya ga kotun da ta kare dimokradiyya.