On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Ta Umarci Gwamnatin Taraiyya Ta Karawa Alkalai Albashi

Mai shari'a Obaseki

Kotun Ma’aikata ta kasa dake zamanta a Abuja babban birnin taraiyya, Ta umarci gwamnatin taraiyya data karawa Alkalai Albashi da kuma sauran hakkokinsu na Alawus, batare da bata lokaci ba.

Mai shari’a  Osatohanmwen Obaseki-Osaghae, ta yanke hukuncin cewa yanayin da Albashin Masu Shari’a da kuma hakkokinsu na Alawus yake a halinsu yanzu, bai tsaya ga iya yin kadan ba, harma da zama wani babban abun kunya.

Kazalika ta baiyana cewa, Kin amincewar da gwamnatin taraiyya tayi na kara albashi da alawus  ga ma’aikatan  shari’a  tsawon shekaru 14 da suka gabata, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma doka.

A bisa haka ne ta umarci gwamnatin taraiyya  data mayar da  albashin  Babban Mai shari’a na kasa a kowane wata akan naira Milyan 10, Sai kuma sauran alkalan kotun Koli da zasu rika tashi da naira Milyan 9, Yayin da shugaban Kotun daukaka kara shima zai rika daukar naira milyan 9, sai kuma sauran Alkalan Kotunan daukaka kara, wadanda zasu rika karbar naira Milyan 8 a matsayin albashinsu na kowane wata.

Sauran sune Alkalan manyan  Kotunan Taraiyya da kuma na jihohi wadanda albashinsu ya koma naira Milyan 8 a yayin da sauran alkalai kuma zasu rika karbar naira Milyan 7 Lakadan a matsayin albashinsu na kowane wata.