On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kotu Ta Umarci Hukumar INEC Ta Wallafa Sunan Sani Yakubu Noma A Matsayin 'Dan Takarar PDP A Arugungu/Augie

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Birnin Kebbi ta umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC da ta wallafa sunan Sani Yakubu Noma a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023.

 

Sani Yakubu Noma ya tsaya takarar zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP na mazabar Argungu da Augie a jihar Kebbi a ranar 25 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki ta 2022 kuma ya yi nasara.

Sai dai PDP ta mika sunan Garba Argugu wanda ya tsaya takarar Gwamnan Kebbi ya sha kaye.

Noma bai gamsu da gabatar da sunan Argungu ba, ta hannun Lauyansa J.J Usman, SAN inda suka  shigar da kara gaban kotun.

Saboda haka kotun ta umurci INEC da ta karba tare da wallafa sunan Sani Yakubu Noma a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Argungu da Augie ta jihar Kebbi a zaben 2023 mai zuwa.

More from Labarai