On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Ganduje Na Hana Yi Masa Binciken Faifan Bidiyon Dala

LAUYA FALANA DA GANDUJE

A ranar 22 ga watan Satumbar bana ne, Kotu zata yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar kano,Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gabanta, na neman ta hana hukumar karbar korafe –korafe da yaki da cin hanci ta jihar Kano yin bincike akansa.

A  jiya  ne  Lauyan  hukumar, Femi Falana SAN,Ya  baiyana cewar rigar  kariyar  da  tsohon  gwamnan ke amfani da ita tazo karshe a ranar  29 ga watan  Mayun bana, A saboda  haka babu wata kotu da zata iya kare shi  ko  iyalansa  ko  kuma  wadanda  ya  yi aiki tare dasu  daga  wani bincike.

To sai dai a martanin da Lauyan Ganduje  ya yi, Ya baiyana  cewar  ba’a ka’idar  data kamata ba,sannan kuma  an take masa  hakkinsa  na Dan adam.

Gwamnatin jihar kano mai ci  a yanzu  dai  ta dauki matakin yin  bincike  kan wani faifan bidiyon Dala  da ake  zargin anga   tsohon gwamnan kano Ganduje na  karbar  cin hancin Dala daga hannun wani Dan kwangila,  Zargin da  tsohon gwamnan ya musanta.