On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kotu Zata Yankewa Sheik Abduljabbar Hukuncin A Makon Gobe

Sheik Abduljabbar

An saka Ranar 15 ga Disambar da muke ciki domin yanke hukuncin kan shari'ar da ake yiwa Sheik Abduljabbar Nasir kabara bisa zarginsa da yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasalam da sahabansa.

Babbar kotun shariar musulunci dake kofar kudu karkashin mai shari'a Ibrahim sarki yola,ta sanya ranar yanke hukuncin akan shari'ar Abduljabbar Nasiru Kabara

Idan ba'a mantaba gwamatin jihar Kano ta gurfanar da Abduljabar gaban kotun shari'ar musulunci bisa wasu tuhume tuhume da ake yi masa wanda suke alaka da batanci ga annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasalam.

An sanya ranar 15 ga wannan wata Disamba da muke ciki domin yanke hukuncin kamar yadda Jami'in hulda da jama'a na kotunan shari'ar  musulinci na jahar Kano Muzammil Ado Fagge ya fitar da sanarwa ga manema labarai da yammacin juma'ar nan.

An dai gurfanar da Abduljabbar agaban kotun tun a watan Yuli na shekarar 2021 ta gabata.