On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotun daukaka kara ta bada umarnin a sake yiwa AA Zaura sabon La-le a Shari'ar zargin damfara

A ranar 9 ga watan Yuni na shekarar 2020 mai Shari'a Honorable Justice Allagoa ya zartas da cewa ba a...

 

Kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Kano  ta jingine hukuncin da wata Babbar Kotun tarayya ta yanke na wankewa tare da sallamar 'Dan takarar gwamnan Kano zaben 2019 Abdulsalam Sale Abdulkarim Zaura wanda ake yiwa lakabi da AA Zaura.

Hukumar yaki da masu yiwa Tattalin Arzikin Kasa zagon Kasa ta EFCC ce ta gurfanar da AA Zaura a gaban Kotu bisa wasu tuhume-tuhume guda 5.

EFCC na zargin zaura da damfarar wani 'dan asalin  Kuwait ta hanyar karbar kudi Dala milliyan 1 da dubu 320 inda ya  yaudareshi da cewar yana kasuwancin Gina gidaje a Dubai da Kuwait da sauran kasashe larabawa.

A ranar 9 ga watan Yuni na shekarar 2020 mai Shari'a Honorable Justice Allagoa ya zartas da cewa ba a samu Zaura da lafin da ake zargi ba.

Sai dai bisa rashin gamsuwa da hukuncin lauyan mai kara  Musa Isah  ya garzaya kotun daukaka kara yana neman a sauya hukuncin.

A wani hukunci ba tare da hamayya ba tsakanin alkalai uku, Mai Shari'a Abdullahi M. Bayero, ya jingine hukuncin Kotun farko.

Ya bada umarnin a sake gurfanar da Zaura a wata sabuwar Shari'a kan batun Amma a wata Kotun ta daban ba Kotun Mai Shari'a Allagoa ba. 

An yanke wannan hukunci ne bisa dogaro da cewa wanda ake zargi bai halarci zaman Kotu ba Lokacin da aka yanke hukunci, hukunce - hukunce da dama da Kotun koli ta yanke na cewa dole Wanda ake zargi ya hakarci zaman Kotu tun daga farko har karshe ciki harda Ranar yanke hukunci saboda wannan ne Kotun daukaka karar ta samu gwarin gwiwar yanke hukuncin.

Mai Shari'a Bayero ya bada umarnin a mayar da karar gaban Babbar Kotun tarayya domin fara sabon La le na Shari'ar.