On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kotun Daukaka Kara Ta Dawo Da Nasarar Hon Datti Na Jam'iyyar NNPP

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a yau Litinin ta warware hukuncin kotun sauraron karrakin zabe inda ta tabbatar da nasarar Yusuf Datti na jam'iyyar NNPP a matsayin dan majalissar tarayya mai wakiltar Kura, Madobi, da Garun Malam.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun karrakin zabe da ya baiwa Musa Ilyasu Kwankwaso na APC nasara.

Idan dai za a iya tunawa INEC ta ayyana Yusuf Datti a matsayin wanda ya lashe zaben wanda Musa Ilyasu Kwankwaso bai gamsu ba, ya kuma garzaya kotu domin kalubalantar nasarar.