On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kotun Daukaka Kara Zata Fara Zaman Shari'ar Karar Da Kungiyar ASUU Ta Shigar Akan Umarnin Kotun Ma'aikata

Yau Talata kotun daukaka kara da ke Abuja zata saurari karar da kungiyar malaman jami’o’I ta kasa  ASUU ta shigar kan hukuncin da kotun ma’aikata ta kasa ta yanke.

 

Kungiyar ASUU ta shigar da dalilai goma sha hudu na daukaka kara kan hukuncin wanda ya umarci malaman da suke yajin aiki su koma bakin aiki har sai an yanke hukuncin karar da gwamnatin tarayya ta shigar ta neman sahihancin yajin aikin na su.

Hakan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin majalisar wakilai da  kungiyar.

Har ila yau, wani rahoto ya ce kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila zai jagoranci wata tawaga a yau domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yajin aikin na ASUU.