On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

kotun Koli Ta Hana Bada Belin Nnamdi Kanu

Nnamdi Kanu

Kotun Koli ta amincewa gwamnatin taraiyya shigar da wasu sabbin tuhume-tuhume guda tara akan karar data daukaka zuwa gaban kotun, inda take kalubalantar hukuncin da wata kotu ta yi na bada umarnin sakin jagoran kungiyar masu fafutikar kafa kasar Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu.

Gwamnatin taraiyya ta hannun lauyanta, Tijjani Gadzali, ta nemi kotun ta bada izinin shigar da sabbin  tuhume-tuhumen da aka yiwa  gyara, cikin kunshin  karar data shigar  gabanta a ranar 28 ga watan Oktoban  2022.

Kotun kolin karkashin alkalai biyar  bisa  jagorancin  John Okoro,  Sune  suka baiwa gwamnatin taraiyyar  damar  a ranar  Alhamis.

A wani bangaren kuma,  A  yayin zaman shari’ar ta Jagoran  kungiyar  IPOB Nmadi Kanu,  Lauyansa Mike Ozekhome,  Ya  fadawa  alkalan kotun  kolin cewar, Daga cikin dalilan da suke son a bada belin Nmadi Kanu hadda magana ta rashin lafiya  da yake fama da ita.

Lauyan ya nemin kotun  da  kodai  ta bada belin Nnamdi Kanu ko kuma ta sake  aikewa  da shi gidan Ajiya da gyaran hali na Kuje,har  zuwa  lokacin da za’a kammala zaman shari’ar da ake masa.

To sai dai a sukar  da  ya gabatar,  Mai gabatar da kara  ya baiyana  cewar wurin da  hukumar tsaro ta farin kaya  DSS ke tsare  da Nnamdi Kanu mai inganci ne, kuma an tanadi duk wani abu da  ya dace  da kula  da lafiyarsa.

Bayan sauraren  bukatar ne,  Kotun kolin ta  shawarci  Lauya Ozekhome dake kare Nnamdi kanu da  ya  janye bukatun  nasa domin samun  saurin gudanar da shari’ar.