On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotun sharia'ar musulunci a nan Kano ta yankewa wani matashi hukuncin zaman gidan kaso, bayan da ya ki ansa lafifin da ake tuhumar sa aikatawa na satar sili

An tasa keyar wani matashi zuwa gidan kaso bisa zargin sa da satar sili a nan Kano

Wata kotun shari’ar musulunci dake Fagge a jihar Kano, tayi umarnin angiza keyar wani matashi mai suna Aminu Surajo dan shekara 18 gidan gyaran hali, bayan da ya ki amsa laifin sa na satar silin rufi da kudinsa ya kai naira dubu 6.

Wanda ake zargin dai dan karamar hukumar Kumbotso ne, an tuhumeshi da laifuka 2.

Alkalin kotun mai shari’a Ismai’l Muhammed Ahmed, bayan sauraron duka bangarori ya dage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan yuni don yanke hukunci.

Tunda fari dai lauyan wanda ake kara Abdul Wada, ya sanar da kotu cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Mayun nan, a unguwar Sheka Gidan Leda, a gidan wani mutum Jamilu Idris.