On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kudirin Masu Bukata Ta Musamman Ya Zama Doka A Jahar Kano - Gwamna Ganduje

Gwamna Abdullahi Ganduje ya rattaba hannu kan kudirin masu bukata ta musamman a jihar Kano na shekarar 2022 inda yanzu ya zama doka.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan amincewa da kudirin dokar a taron majalisar zartarwa na mako-mako, Ganduje ya ce dokar za ta  taimaka wajen tafiya da masu bukata ta musamman da ci gabansu a jihar Kano.

A cewarsa, dokar ta tanadi kafa ma’aikatar da za ta kula da al’amuran masu bukata ta musamman, inda ya kara da cewa dukkanin bangarori shida na masu bukata ta musamman za su samu wakilci a ma’aikatar.

Yace idan aka kafa ma’aikatar, za a ba ta duk wani taimako da ya kamata domin ta yi aiki bisa yadda duniya ke tafiya akai.

More from Labarai