On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kungiyar ASUU Ta Kirawo Taron Gaggawa Bayan Da Aka Zabtare Mata Albashin Watan Oktoba

TAMABARIN GWAMNATIN TARAIYYA DA KUNGIYAR ASUU

Wata sabuwa na neman kara kunno kai a Jami’oin kasar nan, A yayin da kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ke shirin yin wani taron gaggawa na kwamitin kolin kungiyar na kasa.

Duk da cewar ba’a saka  ranar da za’a gudanar da taron ba, rahotanni na baiyana cewa, daukar matakin ya biyo bayan yadda, aka turawa  ‘Yayan kungiyar Malaman jami’oin ta kasa rabin albashinsu na watan Oktoban da ya gabata.
Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodoke  ya tabbatar da cewar  ba’a turawa malaman cikakken albashi ba, a yayin ganawarsa da manema Labarai a Abuja.