On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Kungiyar Hamas Ta Zargi Israila Da Aikata Kisan Kiyashi A Gaza

HAMAS

Shugaban Kungiyar Hamas ta Falasdinawa Ismail Haniyeh ya zargi kasar Isra’ila da aikata kisan kiyashi a yakin da take yi a zirin Gaza, a kokarin na yin ramuwar gaiyya.

Shugaban kungiyar  ya zargi Isra’ila  da aikata lefin kisan ‘kare dangi  akan  fararen hular da babu ruwansu a yakin da ake gwabzawa.

A jawabin da ya gabatar, shugaban kungiyar Hamas  ya yi alkawarin cewar lefukan da Isra’ila  ke aikatawa ba zai kubutar  da ita daga galabar da aka samu akan  tab a.

Hakan na zuwa ne a yayin da a karon farko motocin daukar  marassa lafiya  daga  Gaza dauke da falasdinawa  suka  cikin masar  ta  kan iyakar  Rafah  domin nemar masu magani.