On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kungiyar Kwadago Tayi Biris Da Umarnin Shugaban Kasa Buhari

NLC

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC, Tayi fatali da wa’adin Makwanni biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar domin ganin an kawo karshen yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU, da sauran kungiyoyin dake yajin aiki a Jami’oin, Inda ta jaddada cewa ya zama wajibi ta gudanar da zanga-zangar lumana data shirya gabatarwa a makon gobe.

A yanzu haka kimanin kungiyoyin kwadago 40 ne, cikinsu hadda kungiyar Ma’aikatan Sufurin jiragen sama ta kasa, suka ci alwashin gudanar da zanga-zangar a fadin kasa domin bacin ransu game da gazawar gwamnati wajen biyan bukatun kungiyar ta ASUU.

Kakakin Kungiyar kwadago ta kasa NLC, Mister Benson Upah  ya fadawa manema Labarai a ranar Laraba cewa, gwamnatin taraiyya zata iya kawo karshen yajin aikin a cikin kwana ukku kacal idan da gaske take, inda yace babu makawa  kungiyar zata yi zanga-zangar data tsara.

Kazalika yace wa’adin da aka bawa ministan Ilimi na kasa domin kawo karshen yajin aikin, Ba zai hanasu  gabatar da aniyarsu ba.