On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kungiyar Malamai Ta Bukaci Gwamnatin Taraiyya Ta Aiwatar Da Sabon Tsarin Albashi Da Shugaban Kasa Ya Amince Dashi

Kungiyar malamai ta kaa ta roki gwamnatin taraiyya data gaggauta aiwatar da sabon tsarin albashi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince dashi a shekarar 2021.

Shugaban kungiyar na kasa, Audu Titus ne ya baiyana haka a ranar Laraba, lokacin da yake ganawa da wakiliyarmu  Joy Eberebe, dangane da ranar Malamai ta bana, wadda aka yiwa take da, Cigaban Ilimi yana somawa ne daga Malamai.

A cewarsa sabon tsarin albashin malamai da shugaban kasa muhammadu Buhari  ya amince dashi a yayin bukin ranar Malamai ta bara, har yanzu  ba’a fara aiki dashi ba a matakin jihohi da kuma taraiyya.

Shugaban kungiyar Malaman ta kasa ya baiyana cewa amincewa da sabon tsarin albashin da kuma inganta  walwalarsu  zai temaka wajen bunkasa kwazonsu.