On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kungiyar NARD Ta Dakatar Da Yajin Aiki A Najeriya

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa  NARD ta dakatar da yajin aikin gargadi da take gudanarwa na kwanaki biyar.

Shugaban kungiyar, Dakta Orji Emeka Innocent, shine ya tabbatarwa manema labarai matakin dakatar da yajin aikin da yammacin jiya, inda ya ce likitocin za su ci gaba da aiki da karfe 8 na safiyar yau.

Innocent ya ce za a sake nazari kan ci gaban da aka samu a ranar 2 ga watan gobe na Yuni  yayin babban taron kungiyar inda za a yanke shawara kan mataki na gaba.

Kungiyar ta fara yajin aikin ne a ranar Larabar da ta gabata sakamakon gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatunta bayan cikar wa’adin makonni biyu na kungiyar.

Tunda farko, Likitoci masu neman kwarewar da ke yajin aiki da  kungiyar likitoci ta kasa NMA sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya kan yajin aikin  da aka fara a ranar Laraba.

Kakakin Ma’aikatar Kwadago, Olajide Oshundun, ya bayyana jiya a Abuja cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ofishin ministan ma’aikatar  Chris Ngige a ranar Juma’a.