On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

kungiyar 'Yan Jarida Na Shirin Kai Karar Gwamnatin Jihar Zamfara

TAMBARIN KUNGIYAR YAN JARIDA

Kungiyar Yan Jarida ta kasa tayi barazanar daukar matakin shari’a akan gwamnati da kuma gwamnan jihar Zamfara Bello Matawale, Game da matakin da ya dauka na rufe wasu kafafen yada labarai biyar dake jihar ba bisa ka’ida ba.

A yayin wata hira da aka yi dashi ta cikin shirin daga Dakin Labarai na gidan Rediyon Wazobia,Sakataren  kungiyar na kasa, Shu’aib  Usman Liman, Yace babu wan dalili da zaisa a dauki irin wannan mataki.

Ya kara da cewa gwamnan bashi da hurumin  tauye yancin da kafafen yada labarai suke dashi  duk da kasancewarsa  ta shugaba a jihar.

Liman yace zasu gabatar da batun gaban majalisar tsaro ta kasa domin daukar matakin da ya dace akan lokaci.