On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Kwamitin Amintattu Zai Sake Zaman Neman Mafita Kan Rikicin Cikin Gida Na Jam'iyyar PDP

Mutukar babu wani sauyi da aka samu, kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP zai yi taro a wannan makon domin tattaunawa kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.

Wannan wani babban shiri ne na ceto yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Atiku Abubakar, biyo bayan kauracewa majalissar yakin neman zaben da wasu gwamnonin jam'iyyar suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa majalissar  ba da shawara ta damu da yadda rikicin jam’iyyar da magoya bayan gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ke kara ta’azzara, kuma ana hasashen akwai yiwuwar a bukaci shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu ya yi murabus.

Ko da yake babu cikakkun bayanai game da taron da ranar da za’a gudanar  amma zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, tsohon shugaban kwamitin amintattu Sanata Walid Jibrin, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa sun damu matuka saboda rikicin ya nuna babu alamar samun sauki.