On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kwankwaso Ba Zai Zama Mataimaki Ga Obi Ba - NNPP

Jam'iyyar NNPP ta yi watsi da rahotannin da ke cewa 'dan takarar ta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso zai zama mataimaki ga dantakar Labor Party, Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa.

Bayanin hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam'iyyar, Agbo Mayor ya sanyawa hannu, wacce tace wannan takamaimiyar yarjejeniya bata ta'ba gudana ba tsakanin bangarorin biyu.

"NNPP bata taba cewa dan takarar ta mai girma, Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ka iya amincewa ya zama mataimaki ga Peter Obi na jam'iyyar LP ba."

Ta kuma kara da cewa "ba gaskiya a cikin wannan rahoto kuma abun kunya ne ga jam'iyyar mu, 'dan takarar mu Kwankwaso da kuma miliyoyin magoya bayan jam'iyyar anan Najeriya har ma da kasashen waje, a don haka muke bukatar 'yan jarida da su rika tabbatar da sahihancin labaran da suke wallafawa, gudun kada hakan ya haifar da wani rudani gabannin zaben 2023 mai zuwa."

"Wannan gangami da ya samu goyon baya daga dumbin magoya baya, ya yadda cewa akwai tattaunawa a kasa tsakanin da jam'iyyar LP, domin ganin yadda za'a ceto durkusashiyar demukradiyyar kasar nan," inji Major.

More from Labarai