On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kwankwaso Ya Bayyana Takaici, Yayinda Amnesty Ke Cewa Yawan Mamata Ya Karu Zuwa 12O Sanadiyar Harin Bom Na Sojoji A Kaduna

'Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya bayyana bakin cikinsa kan harin bam da sojojin Najeriya suka kai a daren Ranar  Lahadi a kauyen Tundun Biri dake jihar Kaduna, a yayin bikin Mauludi.

Kwankwaso ya bayyana harin da aka kira na kuskure a matsayin wani babban jigo na gazawar hukumomin tsaro, inda ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da tabbatar da ganin an yi adalci.

Har ila yau, fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da hukunta wadanda suka kai harin bam a kauyukan.

Rahotanni dai na nuni da cewa adadin wadanda suka mutu a al’amarin ya karu zuwa 120 kamar yadda jami’an Amnesty International da suka ziyarci garuruwan  da al’amarin ya shafa suka tabbatar da karuwar adadin wadanda suka mutu.