On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Lafiyata Kalau Ban Janye Daga Takarar Neman Zama Shugaban Najeriya Ba - Bola Tinubu

Yayinda ake tsaka da jefa alamomin tambaya akan yanayin lafiyarsa, Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya musanta zargin da ake yi cewa bashi da lafiya, yana mai cewa yana nan cikin koshin lafiya kuma zai iya jan ragamar shugabancin Najeriya.

 

Ta cikin wani Bidiyo da tsohon gwamna na Legas ya wallafa a shafin Twiter, Tinubu ya musanta Jita-jitar cewa ya janye takarara shugaban shugabancin nkasarnan…

An dai nuna damuwa game da halin lafiyar Tinubu, inda da dama daga cikin ‘yan Najeriya ke nuna shakku kan irin kuzarin  da yake da shi na rike mukami mafi  girma a kasarnan, kasancewar ba a ganinsa  a wani taro na siyasa  a baya-bayan nan.

Sai dai yayin da yake mayar da martani kan tsokacin da akeyi  game da inda Tinubu yake, mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ayo Oyalowo, ya ce dan takarar jam’iyyar yana hutawa a birnin Landan na kasar Birtaniya.