On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Lamidi Apapa Ya Musanta Karbar Milyan 500 Domin Wargaza Jam'iyyar Labour

LAMIDI APAPA

Shugabancin jam’iyyar Labour na kasa tsagin Lamidi Apapa, Ya musanta karbar naira milyan 500 daga hannun wani mutum, domin wargaza karar da jam’iyyar ta shigar a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa.

Da yake  yiwa  manema Labarai jawabi, Jim kadan bayan ya tsallake rijiya da baya  daga  wasu matasa  da suka rika yi masa Ihu jiya a Abuja, Lamidi Apapa, Ya musanta karbar wasu kudi  daga  hannun wani ko wata kungiya  domin yiwa  jam’iyyar zagon kasa.

Ya kara da cewar  ya zama wajibi, Peter Obi ya zama  bashi da wani bangare,  domin warware  rikicin shugabanci da  ya dabaibaye jam’iyyar  a matakin kasa.

Kazalika ya baiyana  ihun da  matasan suka yi masa a  gaban kotun kuma a gaban Peter Obi, a matsayin kaskanci da  kuma  wani  salo  na irin  nagartar  shugabancin da Obi ke  dashi.