On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Likitoci Masu Neman Kwarewa Sunyi Barazanar Tafiya Yajin Aiki

LIKITOCI MASU NEMAN KWAREWA

Kungiyar Likitoci masu neman Kwarewa ta kasa ta bawa gwamnatin taraiyya wa’adin makwanni biyu data gaggauta biya masu bukatunsu, da suka shafi kula da walwalarsu ko kuma ta fuskanci tafiya yajin aiki.

Wata sanarwa mai dauke dasa hannun shugaban Kungiyar na kasa, Dr Dare Godiya Ishaya, Yace likitoci masu neman Kwarewa na bukatar gwamnatin taraiyya ta biyasu sabon alawus na kudaden daukar horo, wanda hakan zai bawa yayansu  kammala abunda ya dace, kafin cikar wa’adin rijistar  jarabawar da suke  rubutawa.

Kazalika sun bukaci gwamnatin taraiyya tayi gaggawar biyansu kudaden  alawus na shiga aiyukan hadari dana ariyas  da dai sauran bukatu.

More from Labarai