On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Macizai Na Saran Fasinjojin Jirgin Kasar Da Aka Sace A Kaduna.

Wani Mai Harkokin Wallafe-Wallafe Mazaunin Jihar Kaduna, Tukur Mamu, Wanda ya shiga tsakanin wajen ganin an sako Mutane 11 daga cikin Fasinjojin da aka sace a yayin harin da aka kaiwa jirgin Kasa a Kaduna, Ya tabbatar da cewa Macizai Sun Sari wasu daga cikin Mutanen da har yanzu suke a hannun ‘Yan Ta’addar.

Malam Tukur Mamu, Ya baiyana haka ne a ranar Litinin, Yayin zantawarsa da Manema Labarai a Kaduna, Yace mutanen sun dogara ne da hanyoyin Gargajiya wajen warkar da ciwon da suka ji, a sakamakon Saran da Macizan suka yi masu, wanda hakan kuma babbar barazana ce ga rayuwarsu.

Kazalika yace rashin bincike akan cututtukan da suke damunsu da kuma rashin samun kulawa, tare da rashin samun abinci mai gina jiki da kuma tabarbarewar wurin da suke a  yanzu, ya kara jefa su cikin halin tagaiyyara.

Daga karshe ya tabbatarwa Iyalan mutanen da aka sace, cewar  babu wani yanayi na cutarwa  da suke fuskanta, Illa  rashin kyawun yanayin wajen da suke a yanzu wanda bai dace dasu ba, Sannan kuma yace gwamnati ce kadai keda ikon  warware matsalar   batare da bata wani lokaci ba.

More from Labarai