On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Mayar Da Kwalejin Sa'adatu Rimi Zuwa Jami'a

KWALEJIN SA'ADATU RIMI

Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da rahoton da kwamitinta mai kula da ilimi mai zurfi ya gabatar, kudirin mayar da kwalejin Sa’adatu Rimi, Jami’ar koyar da fannin ilimi.

Da yake gabatar da rahoton, Shugaban kwamitin, Alhaji Ali Shanono, Yace  kudirin ya tsallake dukkanin wasu matakai da ake bukata in banda mayar dashi doka da ake son yi a halin yanzu.

Shanono, Ya ce daga likafar kwalejin zuwa  jami’ar  zai temaka wajen bunkasa fannin ilimi a jihar nan, sannan kuma zai bunkasa kara samar da zakwakwuran malamai da Dalibai da suka kammala jami’a.

Bayan amincewa da kudirin ne, Majalisar dokokin ta umarci kwamitinta mai lura da fannin bada agajin gaggawa  da ya ziyarci kasuwannin Takai da Singa da aka samu ibtila’in tashin gobara, domin ganin halin da suke a ciki.

A wani bangaren kuma,

Majalisar Dokokin jihar Kano, ta amince  da  Kudirin  mayar da Asibitin  Abdullahi Wase da aka fi sani da Asibitin Nasarawa, zuwa  Asibitin koyarwa.

Matakin ya biyo bayan amincewa da kudirin da shugaban masu rinjaye na zauren majalisar dokokin jihar, Labaran Abdu Madari ya gabatar a gaban majalisar a ranar Talata.

Da yake gabatar da kudirin, Dan majalisar ya baiyana muhimmancin dake akwai na samar da asibitin koyarwa mallakin gwamnatin jihar kano, Yana mai cewa manyan asibitocin da ake dasu a jihar nan sunyi kadan, Sannan ya kara da cewa, Asibitin zai kasance  asibitin koyarwa na jami’ar Yusuf Maitama Sule, wadda  mallakin gwamnatin Kano ce.

Daga bisani majalisar  ta amince da kudirin, bayan yi masa karatu na ukku, da akawun majalisar  Bako Gezawa yayi.