On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Majalissar Dokokin Jihar Kano Ta Zabi Sabon Mataimakin Shugaba

Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi dan majalisa mai wakiltar mazabar Kiru Alhaji Kabiru Hassan Dashi a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Hakan ya biyo bayan ajiye  mukamin da  mataimakin kakakin majalisar Alhaji Zubairu Hamza Massu ya yi Wanda shine dan majalisa  mai wakiltar mazabar Sumaila.

 Jaridar  Solace base ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban majalisar Alhaji Zubairu Hamza Massu, ya koma jam’iyyar NNPP  a kwanaki da suka gabata.

Bayan karanta wasikar a zaman majalissar na ranar litinin, Kakakin majalisar, Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari,  ya  ayyana kujerar mataimakin kakakin majalisar amatsayin wadda ba bu kowa Wanda hakan  ya baiwa dan majalisa mai wakiltar Dawakin Tofa, Hon. Sale Ahmad Marke dama ya zabi Kabiru Dashi a Matsayin sabon mataimakin Shugaban kuma mamba mai wakiltar Wudil Hon. Nuhu Abdullahi Achika ya mara masa baya.

Hon. Kabiru Hassan Dashi, wanda shi ne tsohon bulaliyar majalissar kuma mataimakin shugaban masu rinjaye sannan shugaban masu rinjaye, an amince da ya zama mataimakin kakakin majalisar bayan yan majalisar 28 sun kada masa kuri'a.

Daga bisani kuma daraktan shari'a na majalisar,Barista Nasidi Aliyu ya jagoranci rantsar da shi.

More from Labarai