On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Majalissar Dokokin Najeriya Na Shirin Mikawa Buhari Kudirin Kafa Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya - Peace Corps

Majalisar dokoki ta  kasa ta fara shirin  mikawa fadar shugaban kasa daftarin dokar kafa hukumar wanzar da zaman lafiya ta Najeriya tare da daidaita dokar da majalisun biyu suka yi.

Majalisar wakilai ta jagoranci kafa kwamitin taro na mutum shida da za su yi aiki tare da takwaransu na majalisar dattawa domin daidaitawa tare da samar da tsaftataccen kwafin kudirin da za’a mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari domin amincewa.

Hon. Babangida Ibrahim shine zai jagoranci kwamitin majalisar wakilai yayin da Sanata Kashim Shettima zai jagoranci kwamitin majalisar dattawa.

Ana saran mambobin kwamitin taron zasu duba bambance-bambancen dake tsakani su kuma daidaita su kafin a tura kwafin ga Fadar Shugaban Kasa.