On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Majalissar Wakilai A Najeriya Zata Gana Da Kungiyar ASUU Dake Yajin Aiki A Jami'oin Kasar

Majalisar wakilai za ta gana da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU da sauran masu ruwa da tsaki domin lalubo bakin zaren warware yajin aikin da kungiyar ke yi.

Hakan na kunshe ne a  cikin wata sanarwa da magatakardan majalisar, Yahaya Danzaria ya fitar yau a Abuja. 
Ya ce taron zai gudana ne a gobe Talata a majalisar wakilai ta kasa.
Majalisar ta dauki matakin ganawa da ƙungiyar malaman jami’a da ministan ilimi sakamakon yajin aikin da aka shafe watanni bakwai su na yi.
Takardar gayyatar da aka aikewa kungiyar an bukaci shugabanci da sauran masu ruwa da tsaki su hallara a zauren majalisar gobe domin kawo karshen yajin aikin.
Takardar gayyatar ta nuna yadda ƙungiyar ta nuna damuwarta a dangane da zaman dalibai a gida a sakamakon rashin karatu da ba a yi a mafi yawan jami’a a Najeriya.
Majalisar ta roƙi shugabancin malaman jami’a ASUU da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana a gabanta domin kawo karshen matsalar baki daya.
Tun a karshen mako Gbajibiamila ya kudiri aniyar ganawar da bangarorin da abun ya shafa.