On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Majalissar Wakilai Ta Ayyana Sabon Jirgin Najeriya Amtsayin Damfara

Majalisar Wakilai ta ayyana kaddamar da kamfanin na Nigeria Air amatsayin yaudara bayan da manyan masu ruwa da tsaki a cikin yarjejeniyar suka musanta labarin kaddamar da jirgin.

Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sufurin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya yi Allah-wadai da shirin kaddamar da kamfanin na Nigeria Air wanda aka kaddamar a karshen gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Ma’aikatar sufurin jiragen sama tayi ikirarin cewa an gabatar da jirgin Najeriya Air ne kawai amma ba a kaddamar da shi ba, wanda kwamitin ya yi watsi da hakan amatsayin wani yunkuri na karkatar da hankulan ‘yan majalisar.

Mambobin kwamitin sun yi matukar kaduwa yayin da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya NAMA itama ta bayyana cewa jirgin mai dauke da kalar Najeriya, wani jirgi ne  da aka yi hayarsa zuwa Najeriya.