On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Majalissar Wakilan Najeriya Na Bincike Kan Yadda Hukumomi Suka Kashe Naira Billiyan 447.6 Lokacin Corona

Majalisar Wakilai ta yi sammacin ma’aikatu da  hukumomin gwamnatin tarayya 83 yayin da ta fara bincike kan zargin almubazzaranci da dukiyar gwamnati da ta kai sama da Naira biliyan 447.6 na COVID-19 daga shekarar 2020 zuwa 2022.

Acewar kasafin kudin ma'aikatu da hukumomi akalla 22 daga cikinsu sun samu kasa da Naira billiyan 447.6 a matsayin kudaden tallafin COVID-19 a cikin 2020 kadai.

Hukumomin sun hada da Ma’aikatun Kudi da  Lafiya, Asibitin Kasa da  Abuja  da bangaren Aikin Noma da  Sadarwa da  Matasa da Wasanni, Harkokin Mata da  Ayyukan Jin kai, Hukumar Samar da Aiyuka ta Kasa da kuma hukumar gyran tituna FERMA.

Ma'aikatun za su bayyana a gaban ‘yan majalisar don amsa tambayoyi kan zargin karkatar da kudaden rage radadin COVID-19 da aka raba tsakaninsu don yakar cutar da ta addabi  duniya.