On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Makarantun Firamare da Sakandire A Kano Zasu Fara Hutun Zango Na 2

Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Juma’a 7 ga Afrilu na 2023 a matsayin ranar da za a fara hutun zangon karatu na biyu na watan Ramadan ga ‘Daliban kwana da jeka ka dawo na makarantun gwamnati da da masu zaman kansu na Firamare da kuma sakandire a jihar ta Kano.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Aliyu Yusuf, wadda ya aikowa Arewa Radiyo.

A cewar sanarwar Iyaye za su je domin daukar yaransu a makarantun kwana da safiyar gobe Juma'a.

Hakazalika daliban makarantun kwana za su koma makaranta a ranar Lahadi 30 ga Afrilu, yayin da daliban jeka ka dawo za su koma ranar Litinin 1 ga watan  Mayu na 2023.

Sanarwar ta kara da cewa a yayin nuna jin dadinsa  ga hadin kai da goyon bayan da ake baiwa ma’aikatar, kwamishinan ilimi na jihar Kano Hon. Ya’u Abdullahi Yan-shana ya bukaci iyaye  da su tabbatar da bin ka’idojin da aka amince da su na komawa makaranta.

Kwamishinan wanda ya kuma yiwa dalibai da daliban fatan samun nasara tare da samun hutu yadda ya kamata, ya yi musu fatan kammala Azumin Ramadan lafiya.

Sai dai ya yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka bijirewa ka’idojin komawa akan lokaci.