On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Manjo Hamza Al-Mustapha Yayi Ganawar Sirri Da Gwamna Nyesom Wike Na Jihar Ribas

AL-MUSTAPHA DA GWAMNA WIKE

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance, Hamza Al-Mustapha, a gidansa da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Al-Mustapha wanda ya kasance babban dogarin  Marigayi Janar Sani Abacha wanda ya mulkin kasar nan a  tsakanin  shekarar 1993 zuwa 1998.

Kamar yadda ba’a sanin abubuwan da aka tattauna a ganawar da ake yi tsakanin gwamna Nyesom Wike da wadanda suka ziyar ce shi, haka zalika shima Almustapha ba’a san abubuwan da suka tattauna a tsakaninsu ba.

Babu wani daga cikinsu da ya yi magana da manema labarai bayan kammala ganawar sirrin.

Rahotanni na baiyana cewa  ziyarar  bata rasa nasaba da cigaba da tuntubar juna da ake yi gabanin babban zaben kasar nan dake tafe.

 

More from Labarai