On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Manyan Kasuwannin Jihar Kano Na Bukatar Offishin Kwana-Kwana - Hukumar Kashe Gobara

Yayinda gwamnatin jihar Kano ta cika alkawarin samar da motocin kashe gobara a kasuwar Kantin kwari, sauran manyan kasuwanni da sukagamu da Iftila’in gobara a shekarar da muke ciki na rokon a samar musu da ofisoshin kwana-kwana a kasuwannin nasu.

Arewa Radio ta ganewa idanunta motocin kashe gobara tare da ‘yan kwana-kwana kimanin 20 da aka samar a kasuwar kantin ‘Kwari.

Da wakilinmu Cleb Jecob ya ziyarci kasuwar Kurmi wadda tana daya daga cikin kasuwannni da sukagamu da Iftila’in goba a baya-bayan nan, Sarkin Kasuwar Abdullahi Maikano, yace yanayin cushewar kasuwar yana kawo cikas ga motocin kashe gobara su iya shiga ko ina, sai dai ya roki gwamnati akan hakan.

Maikano ya kara da cewa dagashekarar 2015 zuwa yanzu Kasuwar Kurmi ta gamu da gobara sama da sau 10 ciki harda wadda aka fuskanta a watan Maris na 2023 har shaguna kimanin 80 suka kone.

Anasa bangaren, shugaban kasuwar Singa Ahaji Uba Zubairu Yakasai, koda yake ya yabawa gwamnatin Kano, amma ya zargi wasu mawadata a kasuwar da rashin bada tallafi wajen samar da motar kashe gobara, wanda hakan ya yi sanadin samun gobara sau 3 daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Ita kuwa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta zargi mahukuntan karamar hukum,ar birni da kewaye da kawo cikas wajen tabbatar da offishin kashe gobara da zai dakile yawaitar matsaloli a kasuwar Kurmi.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf Abdullahi,yace a baya akwai offishin kashe gobara a Jakara dake taimakawa kasuwar ta Kurmi sai dai ya zargi shugabancin karamar hukumar birni da karbe  offishin na ‘yan kwana-kwana.

Yace duk lokacin da aka fuskanci gobara sai an taso tawagar motoci da jami’ai daga babban offishin hukumar wanda keda nisa da Kasuwar.

Daga nan ya yi kira ga shugabancin kasuwar da mahukuntan karamar hukumar birni su sake bada damar samar da offishin kwana-kwana a Jakara da zai taimakawa Kasuwar Kurmi da kewaye.