On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Masu Gurkuwa Da Mutane Sun Baiwa Matar Da Suka Sace Dubu 2 A Matsayin Kudin Mota Bayan Sun Karbi Naira Milyan 6

Masu Garkuwa Da Mutane

Wata mai bayar da sheda, Mai suna Hajiya Fatima Ibrahim ta fadawa babbar kotun taraiyya dake zamanta a Zariya cewa, Wadanda suka yi garkuwa da ita sun bata naira dubu 2 a matsayin kudin mota bayan sun karbi naira milyan 6 a matsayin kudin fansa.

Jami’an yansanda na tuhumar wasu mutane da suka ka hada da Dalhatu Shehu da Lawal Aliyu Bullet sai Nuhu Isma’ila da kuma Nura Usmn da hada baki domin aikata lefi, wanda ya hada da fashi da makami da mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya da kuma yin garkuwa da mutane.

Fatima ta baiyana gaban kotun domin bayar da sheda a shari’ar da aka cigaba da yi a babbar kotun jihar Kaduna mai lamba 1 dake zamanta a Dogarawa Zariya,Inda ta ce mutanen sun sace ta ne a ranar  1 ga watan Janairun Bara, Inda suka kaita Dajin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, bayan sun dauke kudi da kayan yaranta da sauran wasu kadarori daga gidanta.

Mai shari’a kabir Dabo ya salami mai gabatar da shaidar, sannan kuma ya dage zaman kotun zuwa ranar 15 ga watan Nuwambar bana domin cigaba da zaman kotun.