On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Masu Ruwa Da Tsaki na Zargin Atiku da Iyorchia Ayu Da Taka Rawa Wajen Rashin Nasara PDP A Zaben Jihar Ekiti

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, da dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, sun fuskanci suka daga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar kan rashin zuwa jihar Ekiti domin yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam’iyyar a zaben ranar 18 ga watan Yuni.

Jiga-jigan jam’iyyar sun ce rashin kulawar da suka nunawa dan takarar gwamnan a zaben Ekiti, Bisi Kolawole, ya taimaka wajen rashin nasarar jam’iyyar a zaben tare da haifar da mummunan zato ga jam’iyyar da dan takararta a zaben Osun.

Kolawole, wanda ya samu kuri’u dubu 67,457, ya zo na uku, yayin da Segun Oni na jam’iyyar SDP ya zo na biyu da kuri’u dubu 82,211, a daidai lokacin da Biodun Oyebanji, na jam’iyyar APC ya lashe zaben da kuri’u dubu 187 da 57.

Gabanin zaben, jam’iyyar PDP a ranar 9 ga watan Yuni ta kafa majalisar yakin neman zabe tunda daga matakin  kasa mai mutane 80, amma 'yan majalisar, kamar Ayu da Atiku, ba su ziyarci jihar don yakin neman zaben dan takarar ba.